9 Disamba 2020 - 15:09
Kotun Koli A Iran Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Ruhullah Zam Dake Kula Da Wani Shafin Yanar Gizo dake adawa da kasar Iran

Kakakin ma’aikatar sharia ta kasar Iran Gulam Muhsin Ismaili a wani taron manema labarai da ya yi, ya bayyana cewa bayan bincike da kotun kolin kasar ta yi game da hukuncin kisa da aka yanke wa Ruhullah Zam wanda ke jagorantar wani shafin yanar gizo dake adawa da gwamnatin kasar Iran daga karshe ta tabbatar da hukuncin.

ABNA24 : An yanke masa hukumcin ne tun a watan Yuni da ya gabata bayan da aka tabbatar da laifin da ake zarginsa da aikatawa na yin leken asiri da kuma fasadi a bayan kasa, kuma dakarun karin juyin musulunci ne suka kama shi a a watan Oktoban shekara ta 2019.

Yana kula da wani shafi ne mai suna Amad New da ya yi kaurin suna wajen cin zarafi jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma musanta Masanan ilimin nukiliyar kasar.

Yanzu haka dai kasar ta dukufa wajen kamo wadanda ke da hannu wajen kashe masanin nukiliyar kasar a baya bayan nan Muhsen Fakhri zade domin yanke musu hukunci.

342/